Lissafin Kuɗi 1

بسم الله الرحمن الرحيم
Assalamu Alaykum, Barkan mu da wannan lokacin.
Kamar yanda kuka sani muna haɗa special Ramadan contribution, wanda Allah ya taimake mu ka hada ₦78,500. Muna godiya da contributions ɗin da kuka bada sosai.
Lissafin Yanda Aka Kashe Kuɗin
Na farko munyi magana da officials akan yanda za ayi da kuɗin wanda kowa ya sani agenda ɗin na ciyarwa ce da taimakawa Marayu da Marasa ƙarfi, sai dai wannan lokacin mun samu issue na marasa lafiya da baya da ƙarfin da za a iya cire mashi haƙori, wanda sana'ar sa faskare ce, sai aka yanke za a taimaka mishi, inda aka kashe ₦12,200 a ɓangaren wankin haƙori da cire wasu daga cikin haƙoran da kuma magunguna da kati.
Wanda kuma mun samu qarin ₦4000 daga hannun wata baiwar Allah wacca ba ƴar kungiya ce ba, tace a ƙara a taimakawa maras lafiyan. Wanda shi ya kama mun kashe ₦8,200 kenan instead of ₦12,200 kenan.
Shi yakama muna da sauran ₦70,300 kenan, wanda muka sai abubuwa kamar haka:
- Shinkafa tiya 9 akan ₦3450, Total= ₦31,050.
- Gero tiya 15 akan ₦1,500, Total = ₦22,500.
- Macaroni 9 akan ₦1000, Total = ₦9,000.
- Taliya 9 akan ₦850, Total = ₦7,650.
Total = ₦70,200.
note: Zirga zirga free.
Zuwa yanzu an yanke za a taimakawa gidaje 3 na marasa ƙarfi ko marayu, wanda zuwa yanzu anyi ɗaya na maras ƙarfi kuma da maras lahiya.
Alhamdulillahi muna godiya ga Allah da ya bamu iko da hali da zuciya na taimakon bayinsa musulmai, muna ƙara godiya ga gudumowar ku, Allah qara sakawa kowa da alkhairi.