Lissafin Kuɗi 2

بسم الله الرحمن الرحيم
Assalamu Alaykum Warahmatullahi Wabarakatuhu,
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah (SWT) Ubangijin kowa da komai, tsira da aminci su tabbata ga Annabin Rahma Annabi Muhammad (SAW), bayan haka munawa kowa fatan alkhairi.
Kamar yanda muka bada sanarwa kwana takwas da saka wuce, akan cewa ƙungiya ta bada damar duk wanda yake da wanda za'a taimakawa ko yasan waɗanda suke da matsananciyar buƙata ko wata irice, to ya kawo ƙorafin shi zuwa ga ƙungiya a duba a gani insha Allahu za'a taimaka.
Toh mun samu wasu bayin Allah mutum biyu waɗanda suke cikin wannan ƙungiya tamu mai albarka, sunzo mana da koken wasu bayin Allah waɗanda suke da tsananin buƙatuwar a taimaka musu, kuma cikin ikon Allah da yardarsa da amincewarsa ansamu nasarar taimaka musu.
Ga yadda lissafin ya kasance, an sayi:
- Shinkafa tiya (6) akan ₦2,900 per tiya, Total= ₦17,400.
- Masara tiya (10) akan ₦1,150 per tiya, Total= ₦11,500.
- Wake tiya (2) akan ₦2,500, Total= ₦5,000.
- Taliya guda (6) akan ₦900 per each, Total= ₦5,350.
- Macaroni guda (6) akan ₦950 per each, Total= ₦5,700.
- Sai kuma dubu goma goma ₦10,000 da aka basu don su ƙara jari.
Total amount da aka kashe shine, naira dubu sittin da biyar da naira hamsin(₦65,050).
Daga ƙarshe muna ƙara tunatar da junanmu faɗar manzon Allah (SAW) cewa {Allah yana taimakon bawa matuƙar bawa yana taimakon ƴan uwansa}. Allah bamu ikon taimakawa kuma Allah sakawa kowa da Alkhairi.