January 14, 2026
Lissafin Kuɗi 3

بسم الله الرحمن الرحيم
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, muna yiwa kowa da kowa Barka da wannan lokaci mai albarka.
Muna ƙara jaddada godiyar mu ga Allah (SWT), tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW).
Bayan haka, kamar yanda kuka sani cewa daga cikin dalilan kafa wannan ƙungiyar akwai taimakawa marasa ƙarfi.
Sabida haka a satin daya wuce, wannan ƙungiyar tamu mai albarka ta gabatar da project ga wani dattijo da yake cikin matsananciyar buƙatar taimako shi da iyalansa domin gudanar da rayuwarsa ta yau da gobe.
Ga yanda lissafin ya kasance, an sayi:
- Masara tiya (7)
- Shinkafa tiya (4)
- Wake tiya (2)
- Taliya guda (5 )
- Macaroni guda (5)
- Maggi leda (1)
Total= ₦29,700
Allah biya ya sa mana Albarka.